BBC navigation

An kashe dan sanda daya a Mombasan Kenya

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:11 GMT
Matasa masu zanga-zanga suna kona tayoyi a kan titunan Mombassa

Matasa masu zanga-zanga suna kona tayoyi a kan titunan Mombassa

An kashe wani dan sandan kasar Kenya, an kuma raunata wadansu goma sha shida a rana ta biyu ta tarzoma a birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa.

Rahotannin na cewa wadansu matasa Musulmi sun jefa gurneti a kan ’yan sandan.

An washashe shaguna, sannan aka banka musu wuta; an kuma rika harba hayaki mai sa hawaye.

Tarzomar dai ta biyo bayan kashe wani malamin addinin Musulunci ne, Aboud Rogo Muhammad, wanda ke cikin jerin mutanen da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka kakabawa takunkumi, bayan an zarge shi da tura mayaka da kuma gudunmawar kudi ga mayakan sa-kai na Al-Shabaab a Somalia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.