BBC navigation

Obama ya gargadi mutanen New Orleans game da guguwar Isaac

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:20 GMT
Shugaba Barack Obama

Shugaba Barack Obama

Shugaba Obama ya gargadi jama'a dake zaune a gabar tekun Amurkar da su dauki matakan kariya, yayinda wata mahaukaciyar guguwa hade da ruwa ke shirin ratsawa ta jihar New Orleans.

Mr Obama na magana ne jim kadan kafin a bada sanarwar cewar karfin mahaukaciyar guguwar ya karu.

A cikin daren yau ake sa ran mahaukaciyar guguwar zata isa can, yayinda ake cika shekaru bakwai da mahaukaciyar guguwar Katrina ta fada wa yankin , inda ta halaka mutane sama da dubu daya da dari takwas.

Shugaba Obama ya ce "Muna fuskantar iska da ruwa masu karfin gaske, kuma za a iya samun ambaliya mai yawa da ma sauran barna a cikin yanki mai dama.Yanzu ba lokaci ne na daukar kaddara ba.Yanzu ba lokaci ne na yin watsi da gargadin jami'ai ba. Ya kamata ku dauki wannan da gaske."

Ya ce, jami'an tarayya sun kasance a can tun mako guda, suna shirya wa zuwan mahaukaciyar guguwar.

Da ba don mahaukaciyar guguwar ta Isaac za ta doshi New Orleans kai tsaye ba sannan kuma yau da gobe ranaku ne na tunawa da barnar mahaukaciyar guguwa Katrina -- wadda ta kashe mutane fiye da dubu 1800 -- mai yiwuwa da Shugaban bai yi magana ma baki daya ba.

To amma rashin martani mai kwari daga gwamnatin Bush a kan mahaukaciyar guguwar ta Katrina ya haifar da matsalar siyasa mummuna kuma wannan shugaban yana sane da cewar dole ya a ga yana tare da jama'ar.

Ana sa ran mahaukaciyar guguwar ta Isaac ta sauka a wani lokaci cikin dare, a lokacin da za a iya daga girmanta zuwa mataki na daya.

A fili take dai cewar cewar wannan ba za ta kasance da girma kamar Katrina ba, to amma wani hadin ruwa da iska mai karfi gaske ka iya haddasa babbar ambaliya a gabar teku.

Wani wakilin BBC ya ce shugaba Obama na so ya nuna yana sa ido kan abubuwan dake faruwa , a daidai lokacin da ake gabatar da abokin hamayyarsa na jam'iyar Republican, Mitt Romney , a matsayin dan takarar shugaban kasa, a babban taron jam'iyyar da ake gudanarwa a Tampa, Florida dake gabar teku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.