BBC navigation

Turkiya ta dage kan kafa tudun mun tsira ga yan gudun hijira a Syria

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:13 GMT
Ahmet Davutoglo , Ministan harkokin wajen Turkiya

Ahmet Davutoglo , Ministan harkokin wajen Turkiya

Kasar Turkiyya na ci gaba da matsa lambar ganinmajalisar dinkin duniya ta shata wani yanki na tudun-mun-tsira a Syria, domin tsugunar da 'yan gudun hijirar Syriar dake guje ma tashin hankalin da ake yi.

Ministan harkokin wajen Turkiyya, Ahmet Davutoglu, ya ce zai sake tayar da maganar gobe, Alhamis, a gaban kwamitin sulhu na MDD.

Ya ce, "idan yawan 'yan gudun hijira ya kai dubu dari, ko duban daruruwa, matsalar ta wuce rikicin cikin gida, ta kuma matsalar da ta shafi kasashen duniya."

Turkiyya ta tsugunar da 'yan gudun hijira dubu tamanin, ta kuma ce lamarin na neman ya fi karfinta.

Sai dai a wata hira da za a watsa a wani gidan talabijin mai goyon bayan gwamnati, Mr Assad ya ce batun shata irin wannan yanki na mun-tsira ma bai ko taso ba.

A halin da ake ciki kuma, Kafafen yada labaran Syria na bada rahotannin cewa dakarun kasar sun fatattaki wasu 'yan tawaye da suka kai farmaki a wani sansanin mayakan sama dake garin Taftanaz, inda suka yi masu barna mai yawan gaske.

Kafin haka, dakarun 'yan tawaye sun ce sun lalata jiragen yaki masu saukar angulu da dama a filin jirgin, ta hanyar amfani da wasu tankokin yaki biyu da suka kwace. Babu dai wata majiya mai zaman kanta da zata tabbatar da sahihancin labarin.

Sai dai wasu yan gwagwarmaya a yankin sun sa wasu hotunan video a intanet dake nuna helikoftocin da suka ce sun lalata.


A halin da ake ciki kuma, masu fafutukar sun ce an kashe mutane goma sha daya, a wani fada a wasu anguwanni dake wajen birnin Damascus, daga bangaren gabas.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.