BBC navigation

Kowa ya mallaki bilyoyin da aka karba daga hannun James Ibori?

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:26 GMT
James Ibori

Batun ko wanene ya mallaki wasu kudi dala miliyan goma sha biyar da aka gabatar a gaban kotu ya koma wani abu mai sarkakiya.

Ana zargin tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori da baiwa tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati ta Najeriya,

Malam Nuhu Ribadu, toshiyar baki game da tuhumar da ake masa da yin sama da fadi da kudaden gwamnatin jihar Delta a shekara ta 2007.

Kotun ta bada wa'adin kusan wata daya ga duk wani dake ikirarin cewa kudin nasa ne a kan ya bayyana a gabanta kuma ya zuwa yanzu an samu bangarori uku dake ikirarin cewar kudin nasu ne.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.