BBC navigation

Shugaba Assad ya ki amincewa da shata yankin tudun mun- tsira

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:35 GMT
Shugaba Asaad na Syria

Shugaba Asaad ya ki amincewa da shawarar Turkiyya

Shugaban Kasar Syria , Bashar Al-Assad ya yi watsi da shawarar da aka bayar cewa a tsugunar da 'yan gudun hijirar Syria, a wani yanki na tudun mun-tsira da za a shata a cikin kasar.

A wata hira da za a watsa a wani gidan talabijin mai goyon bayan gwamnati, Mr. Assad ya ce batun shata irin wannan yanki na mun-tsira , wanda Turkiyya ke bada shawara a kai , bai ma taso ba.

Ya kuma yabawa dakarun Kasar ta Syria.

Shugaban ya ce 'ina shaida ma al'ummar Syria cewa, makomar Syria na hannun ku, kuma sojoji da 'yan sanda da ma sauran jami'an tsaro na gudanar da ayyukan su'.

Mr. Assad ya bayyana sauya sheka da wasu jami'an gwamnmatin Syrian su ka yi da cewa, wasu bara-gurbi ne, su ka rufa wa kansu asiri, su ka san inda dare yayi masu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.