BBC navigation

Jama'iyar NDC ta zabi Shugaba Mahama a matsayin dan takararta

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 21:03 GMT
Shugaba John Dramani Mahama na Ghana

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana na ratsuwar kama aiki

Jama'iyar NDC mai mulki a kasar Ghana ta zabi, Shugaban rikon kwarya, John Dramani Mahama a matsayin dan takararta a zaben Shugaban kasar da za a yi cikin watan Disamba tare da fatan kusan kuri'ar baki dayan da aka kada masa za ta farfado da hadin kai a Jama'iyar bayan watanni na fadan cikin gida.

Shugaba Mahama, wanda ya maye gurbin tsohon Shugaban kasa Marigayi, John Atta Mills a matsayin shugaban kasar dake da arzikin Cocoa da zinari da kuma mai,shi ne Jama'iyar ta dauri aniyar dorawa, to amma dole sai da wata kuri'a a babban taron jama'iyar ta tabbatar da shi a Kumasi.

Ya samu kashi casa'in da tara da rabi cikin dari na yawan kuri'un da aka kada a zaben da jama'iyar take fatan zai cike barakar da galibi ta dogara a kan kalubalantar shugabancin da Uwargidan tsohon Shugaba kasa Jerry Rawlings ta yi.

Ana sa ran Mahama zai fuskanci babban kalubale daga dan takarar jama'iyar adawa ta NPP, Nana Akufo-Addo.

Manyan jami'an Jama'iyar ne suka halarci babban taron jama'iyar NDC din dai da aka yi a Birnin Kumasi , birni na biyu a girma a kasar ta Ghana kuma inda jama'iyar NPP take da karfi, sanye da tufafin makoki don tunawa da Marigayi Shugaba Atta Mills.

A cikin yan watannin nan dai akwai rade radin cewar Rawlings mai shekaru 65 wanda kuma ya kankane siyasar kasar Ghana na tsawon shekaru 20 bayan juyin mulkin 1979 sannan kuma ya zabi Mills don karbar ragamar jama'iyar NDC a 2000, zai janye ya kafa tasa jama'iyar.

To amma ya je wajen taron kuma ya bayar da goyon bayansa ga Mahama, inda ya bukace shi da ya farfado da mutuncin shugabancin kasar da Gwamnati da kuma jama'iyar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.