BBC navigation

Gubar dalma ta kashe yara biyu a Gusau, Najeriya

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:49 GMT
Wata mahaka zinare a Najeriya

Wata mahaka zinare a Najeriya

Rahotonni daga Gusau, babban birnin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, na cewa an samu akalla yara biyu sun mutu sakamakon ta’ammuli da gubar dalma.

Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Mohammed Kabir Danbaba, shi ne ya sanar da faruwar al’amarin a gidan rediyon Jihar ta Zamfara, bayan da binciken wadansu kwararrun likitoci ya tabbatar da cewa yaran biyu sun mutu ne sanadiyyar kamuwa da cutar gubar dalmar.

Wata majiya a fadar sarkin ta tabatar wa BBC hakan.

Babban jami'in kungiyar likitoci ta Medecine sans Frontiere da ke aiki a arewacin Najeriya, Ivan Gaetan, ya bayyana cewa, “Sama da mutane dari hudu sun mutu a baya; abin da mu ke gani a yanzu shi ne mahakan zinare na gargajiya na ci gaba da bunkasa tare da gudanar da aikin hakar zinare a cikin gidajen su. Muna fargabar cewa akwai hadarin mutane da dama za su kamu da wannan guba a Jihar ta Zamfara”.

Ya kuma kara da cewa: “Ina ganin abin da ya faru a wannan karo shi ne mutane [kan] dauko duwatsu suna zuwa da su gida ko cikin gari domin yin aiki a kan su; [hakan ne] ya kawo yaduwar gubar—ganin cewa zinare na da kudi yanzu a kasuwannin duniya”.

A shekarar 2010 daruruwn yara sun mutu a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke Jihar ta Zamfara sanadiyar taammali da gubar ta dalma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.