BBC navigation

An harbe dakarun NATO biyar a Afghanistan

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:16 GMT

Sojojin NATO a Afghanistan

Wani dan bindiga ya harbe dakarun kungiyar tsaro ta NATO guda uku har lahira, yayin da wasu biyu suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sama a kasar Afghanistan.

Ma'aikatar tsaron Australia ta tabbatar da cewa sojojin nata ne, sai dai ba ta yi karin bayani ba.

Ana samun karuwar yawan hare-haren da sojojin Afghanistan ke kai wa takwarorinsu na kasashen waje, inda ya zuwa yanzu aka kashe sojoji arba'in a bana idan aka kwatanta da talatin da biyar da aka kashe a bara.

A makon jiya, shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana matukar damuwarsa game da yawan kashe sojojin kasashen waje da ake yi a Afghanistan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.