BBC navigation

Abromovitch ya kayar da Berezovsky a kotu

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:59 GMT
Abramovich da Berezovsky

Abramovich da Berezovsky

Fitaccen dan kasuwar nan, Boris Berezovsky, bai yi nasara ba a shari'ar da ya jima yana fafatawa tare da mutumin da ya mallaki kulab din Chelsea, Roman Abramovich, bayan da wata kotu a nan London ta yi watsi da ikirarin Mr Berezovskyn.

Dukkansu hamshakan attajirai ne 'yan asalin kasar Rasha.

Mr Berezovsky, wanda ke zaman gudun hijira a Birtaniya, ya nemi diyya ce ta bilyoyin daloli a kan wani ciniki da suka yi a shekarun 1990.

Mai shari'a ta yi watsi da karar ne, tana bayyana Mr Berezovsky a matsayin wanda ba za a iya amincewa da shedarsa ba, saboda daukar gaskiya da ya yi a matsayin abar da za a iya lankwasawa.

Jim kadan bayanda da aka yanke hukuncin, Mr Berezovsky ya ce ba shi da kwarin gwiwa akan yadda tsarin shari'ar Ingila yake, amma duk da haka bai yi nadamar matakin da ya dauka ba.

Da ma dai abinda suke ja'in'ja a kai, shi ne cewa Mr Boris Berezovsky ya zargi Mr Abramovich da tilasta masa cefanar da wani katafaren kamfaninsa na mai a farashi dan kadan, abinda ya janyowa Mr Beresovsky din ya tafka dimbin hasara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.