BBC navigation

Kofi Annan ya kammala aikinsa a Syria

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:29 GMT
Kofi Annan

Kofi Annan

A ranar Juma'a ne Kofi Annan ke kammala aikinsa a matsayinsa wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa a kan kasar Syria.

Wasu na cewa aikin da aka baiwa Kofi Annan ba zai taba yiwuwa ba,amma da farko kamar za a iya cewa ya samu nasara.

Bayan an kwashe watanni ana samun baraka, yayi kokarin hada kwan 'yan kwamitin sulhu an MDD sun amince da sharuddan da ya gindaya na samar da zaman lafiya a Syria, da kuma tsarin siyasa wanda zai tabbatar da mika madafan iko a Syriar.

Duka gwamnati da 'yan adawar Syriar dai sun yi na'am da wannan mataki.

Sai dai abin da ya gagare shi ne shawo kan wakilan kwamitin su amince da yadda makomar Bashar al-Assad zata kasance.

Tsakanin kasashen yammacin duniya wadanda ke cewa kawar da shugaban kasar daga mulki na daga cikin sharuddan mika mulki, a daya bangaren kuma Rasha da China na cewa zasu amince da hakan ne kawai idan al'umar Syriar ce ta yanke hukuncin haka wajen tattaunawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.