BBC navigation

Lauyoyi a Afrika ta Kudu suna neman sakin mahaka ma'adinai da ake tuhuma da laifin kisan kai

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
Mahaka ma'adinan Afrika ta Kudu

Ana jiran jin ta bakin masu tuhuma

Lauyoyi a Afirka ta Kudu na barazanar daukar matakin shari'a a madadin mahakan ma'adinai su dari biyu da saba’in, wadanda ake zargi kisan abokan aikinsu guda talatin da hudu.

‘Yansanda ne dai suka harbe wadannan abokan aikin mahaka ma’adinan.

Lawyoyin dole ne a sako mahaka ma'adinan da ake tsare da su, nan da gobe Lahadi, ko kuma suka ce su daukaka kara zuwa babbar kotu domin ta ba da umurnin a sake su.

Ana dai tuhumar Ma'aikatan ne a karkashin wata doka ta zamanin wariyar launin fata

Joseph Mathunjwa shi ne shugaban kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai da gine-gine, ya kuma ce, “Abin ya zo min da mamaki.

“Ta yaya za ka tuhumi mutanen da ba su yi harbe mutanen da bindiga ba, wadanda kuma babu shaidar cewa sun kashe kowa, a kuma bar 'yan sanda?

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.