BBC navigation

An yi zanga-zanga saboda karancin lantarki a Najeriya

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:37 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Al'ummar garin Tambuwal da ke Jihar Sokoto a arewacin Najeriya sun gudanar da wata zanga-zanga ta lumana domin nuna rishin jin dadinsu da kwauron wutar lantarki da su ke fuskanta.

Al'ummar sun koka ne da rashin wadatacciyar watar lantarki daga kamfanin kula da samar da watar lamtarki ta kasa, wato PHCN.

Kakakin al'ummar, Shehu Abba Tambuwal, ya shaidawa BBC cewa:

“Ya kamata a ba mu wuta awa dari bakwai da ashirin a wata guda; aka dawo aka ce za a ba mu awa dari uku da sittin; ba ta samu ba aka ce awa dari da tamanin; ba ta samu ba—da watan azumi gaba daya wutar awa talatin da bakwai muka samu da minti arba’in da hudu”.

Ya kuma kara da cewa sakamakon haka, ba za su biya kudin wuta na watan ba, “don ba mu sha ba—ba ka biyan abin da ba ka saya ba”.

A nasa bangare, kamfanin samar da wutar lantarkin na PHCN ya ce babu dalilin da zai sa mutane su ki biyan kudin wutar da aka ba su, tunda dai ba kyauta ake bayarwa ba.

A cewar Lawali Shinkafi, jami'in kamfanin mai kula da sashen kasuwanci a shiyyar Kebbi, “muna [bayar da wuta] daidai gwargwado; abin da ke faruwa, layin yana da tsawo ne—lodi ya masa yawa—lokacin duk da aka samu matsala a wani kauye sai ka ga layin layin ya dauke: da ba ma kokari ba za ma su ga wutar ba”.

A Najeriya dai maganar samar da wadatacciyar wutar lantarki ga jama'ar kasar na kwan-gaba-kwan-baya shekara da shekaru.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.