BBC navigation

'Yan tawayen Mali sun kame muhimmin garin Douentza

An sabunta: 2 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:46 GMT
Mayaka 'yan kishin Islama na kasar Mali

Wasu mayaka 'yan kishin Islama na kasar Mali

Mayaka 'yan Kishin Islama a kasar Mali sun karbe garin Douentza inda suka kara fadada yankunan da suke rike da iko da su a kasar.

Wasu mazauna garin dai sun ce an dan samu turjiya daga wasu 'yan bingida dake garin, kafin daga bisani mayaka 'yan kishin Islaman da ke ikirarin tabbatar da hadin kan Musulmi a Mali suka kwace iko a garin.

Garin na Douentza dai na da matukar muhimmanci kasancewar ya sa mayakan kara kusantowa da tsakiyar kasar da gwamnatin Mali ke rike da iko.

Mazauna garin sun ce sun ga wani jerin gwanon manyan motocin Jeep-Jeep dauke da 'yan tawayen masu dogon gemu sun shiga garin da safiyar ranar Asabar.

Matsin Lamba

Kasar ta Mali dai kafin wannan shekarar ta kasance daya daga cikin kasashen da ke da zaman lafiya, sai dai tawayen da Abzinawa suka yi a arewacin kasar da kuma juyin mulkin sojoji a kudancin kasar ya yi lahani ga zaman lafiyar Mali.

Sakamakon matsin lamba daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, sojoji sun mika mulki ga fararen hula.

An kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa a watan Agusta wadda aka daura wa alhakin kawo karshen rashin zaman lafiya a arewacin kasar.

Ita ma kungiyar ECOWAS ta ce za ta tura dakaru 3,000 zuwa Mali domin su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.

A watan Agusta shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi gargadin cewa, matukar ba a cimma matsaya da 'yan tawayen Mali ba, to babu makawa sai an yake su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.