BBC navigation

An yi jana'izar Firayim Minista Meles Zenawi

An sabunta: 2 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:14 GMT
Gawar Meles Zenawi yayin da ta isa majami'ar da za a binne shi

Gawar Meles Zenawi yayin da ta isa majami'ar da za a binne shi

Ana ci gaba da jimamin rashin Firayim Ministan Habasha, Meles Zenawi, wanda aka yi jana'izarsa ranar Lahadi a birnin Addis Ababa, aka kuma rufe shi a makwancinsa da ke wata babbar majami'a ta birnin.

Shugabanni daga kasashen duniya da suka halarci jana'izar sun hada da Goodluck Jonathan na Najeriya, da Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, da Boni Yayi na Jamhuriyar Bini—wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka.

Da dama daga cikinsu, kamar su Shugaba Paul Kagame na Rwanda, sun jinjinawa marigayin.

Mista Kagame ya ce margayi Meles Zenawai ya sadaukar da kai wajen ganin cewa nahiyar Afirka ta ci gaba.

Dubban 'yan kasar ta Habasha sanye da bakaken kaya da ke dauke da hotunan marigayi Meles Zenawi ne suka fito suna jimamin rashinsa.

Meles Zenawi ya kasance babban abokin Amurka a yakin da take yi da ta'addanci a yankin kusurwar Afirka.

Ana danganta ci gaban da kasar Habasha ta samu a 'yan shekarun nan ga Meles Zenawi, amma kuma ana sukarsa saboda da tauye hakkin bil-Adama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.