BBC navigation

An bayyana ka'idojin takarar shugabancin Somalia

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:49 GMT
Mohamed Osman Jawaar

Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Somalia, Mohamed Osman Jawaar

Kwamitin shirya zaben shugaban kasa a Somalia ya ce ya fara karbar takardun wadanda ke son tsayawa takara.

Majalisar dokokin kasar ta Somalia ce ta kafa wannan kwamiti don ya shirya yadda za a gudanar da zaben na shugaban kasa.

Mai magana da yawun kwamitin, Osman Libaah, ya shaidawa Sashen Somali na BBC cewa a cikin kwanki uku masu zuwa za su raba takardar ta tsayawa takara.

Ya kuma yi bayanin ka'idojin da duk dan takara zai cika:

“Dole ne dan takara ya kasance dan asalin kasar Somalia, kuma Musulmi mai cikakken koshin lafiya da kyakkyawar zuciya.

“Dole ya zama mai ilimi da kuma kwarewar aiki, tare da sanin yadda zai gudanar da aikinsa yadda ya kamata a matsayinsa na shugaban kasa. Kuma dole ya kasance ya haura shekaru arba’in da haihuwa”.

An kuma shaidawa ’yan takarar cewa sai sun ajiye wa kwamitin kudi dala dubu goma.

Masu sharhi sun ce wadansu ’yan takarar za su wahala kafin su hada wannan kudi, da kuma samun sa-hannun ’yan majalisar dokokin kasar ashirin kamar yadda kwamitin ya bukata.

Ya zuwa yanzu dai fiye da ’yan takara ashirin da biyar ne suka nuna sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasar, amma babu tabbas a kan nawa ne daga cikin su suka cika wadannan ka'idoji.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.