BBC navigation

An ci tarar kamfanonin sadarwa a Nijar

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:33 GMT
Shugaba Issoufou na Nijar

Shugaba Issoufou na Nijar

A jamhuriyar Nijar, an ci tarar wasu kamfanonin sadarwa masu zaman kansu, bisa zargin rashin cika alkawuran da suka dauka a lokacin ba su lasisi.

Hukumar kula da kamfanonin da gwamnatin ta sayar, domin kare hakkin gwamnati da na jama'a, ARM, ta zargi kamfanonin da aikata zamba cikin aminci ga masu layukan wayar salula, da kuma almundahana.

Kamfanonin wayar salular da aka ci tarar a Nijar su ne:

Celtel Niger- sama da bilyan 2 na CFA, da Sahelcom- sama da miliyan 74, sai kuma Sonitel- Sama da miliyan dari 3 na CFA.

Sauran sun hada da Orange Niger-sama da miliyan 800 na CFA, da kuma Atlantic Telecom ko Moov Niger- sama da miliyan dari biyu.

Hukumar ta ARM ta ba su kwanaki sha biyar domin su biya wadannan kudade.

Wasu 'yan Kasar ta Nijar dai sun yi marhabin da matakin.

An nemi jin martanin kamfanonin da abin ya shafa, amma sun ce sai sun kammala nazarin matakin kafin su fitar da matsayinsu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.