BBC navigation

An saki mahaka ma'adinai da ake tuhuma a Afrika ta Kudu

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:26 GMT
Mahaka ma'adinai

Har yanzu ba a wanke su ba tukuna

Wata kotu a Afrika ta Kudu ta saki wasu ma'aikatan ma'adinai , bayan da aka yi watsi da tuhumar da ake yi masu ta aikata kisan kai.

An tuhume su ne bayan da 'yan sanda suka bude wuta cikin mahaka ma'adinan dake zanga zanga, a mahakar ma'adinai ta Marikana a watan jiya.

Wannan lamari ya haddasa mutuwar mutane talatin-da-hudu, wasu kuma sama da haka suka ji raunuka.

An tuhume su din ne karkashin wata doka ta zamanin mulkin wariya, wadda ke cewa, idan aka tunzura 'yan sanda suka aikata wani abu, laifin na wuyan mahaka ma'adinan.

Musabbabin rikicin dai shi ne yajin aikin da mahakan na kamfanin Lonmin suka shiga wani yajin aiki da zummar neman kariin albashi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.