BBC navigation

Takaddama kan gubar dalma a jihar Zamfara

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:34 GMT
Mahakar zinari a jihar Zamfara, Najeriya

Wasu na aikin hakar zinari a jihar Zamfara, arewacin Najerya.

Ana ci gaba da sa in sa game da batun sake bullar cutar gubar dalma a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya.

An dai samu bayanai masu karo da juna dangane da batun bullar cutar gubar dalmar a wadansu yankunan na daban a jhar Zamfarar, inda a yanzu gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa wasu wurare a garin Gusau babban birnin jahar sun gurbata da gubar.

A makon jiya ne dai gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan watsa labarai ta musanta cewar an gano sabbin wurare hudu da cutar gubar dalmar ta bulla, baya ga wasu yankunan Anka da Bukuyum da aka riga aka sani.

Daga bisani ne dai Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar ta sake fitar da bayanan cewa akwai gubar ta dalma a wadannna wuraren.

Wannan dai ya biyo bayan da Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji Kabir Danbaba yayi wani jawabi ta kafafen watsa labarai domin ankarar da hukumomi cewar an samu bullar cutar a masarautar sa kuma har ta hallaka yara biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.