BBC navigation

An kashe mutane da yawa a Afghanistan

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:26 GMT
Harin dan kunar bakin wake a Afghanistan

Harin dan kunar bakin wake a Afghanistan

Wani dan kunar bakin wake a gabashin Afghanistan ya hallaka mutane akalla ashirin da biyar, sannan ya raunata wasu mutanen hamsin.

Dan kunar bakin waken ya kai harin ne a lokacin wata jana'izar da daruruwan mutanen wani kauye ke halarta, da suka kuma hada da Gwamnan Lardin da kuma iyalan mamacin.

Jami'an yankin sunce akwai yiwuwar kungiyar Taliban ce ta kaddamar da harin a matsayin wani martani game da wani bore da mutanen yankin suka yi kwanaki uku da suka gabata, domin nuna kin jinin kasancewar su a yankin.

Sai dai Kungiyar Taliban din ta ce ba ita ta kai harin ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.