BBC navigation

Shugaban Colombia ya bayyana shirin samar da zaman lafiya a kasar

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Shugaba Juan Manuel Santos na Colombia

Shugaba Juan Manuel Santos na Colombia

Shugaban kasar Colombia , Juan Manuel Santos ya fitar da cikakken bayani kan tattaunawar sulhun da aka tsara shiga da kungiyar 'yan tawaye ta FARC, wadda ita ce mafi girma a kasar.

Wannan ne muhimmin yunkuri na farko cikin shekaru goma, na samo hanyar warware rikicin da aka shafe shejara da shekaru ana fama da shi.

Za a fara tattaunawar ce a kasar Norway, kafin a koma Cuba .

Shugaban Colombian yace yayi imanin cewar akwai dama ta zahiri na kawo karshen rikicin 'yan tawayen

Tare da samun takin bayan Kwamnadojin dakarun tsaro da yansandan Colombia, Shugaba Santos ya bukaci Yan Colombia da su baiwa yunkurin samar da zaman lafiyar dama.

Ya ce, a matsayinsa na Shugaban kasa, wannan wata dama ce da ba zai bari ta wuce ba, musamman tare da yin la'akari da miliyoyin mutanen da suka sha wuya sakamakon shekaru 50 da aka kwashe ana yakin.

Mr Santos ya ce yunkurin samar da zaman lafiyar ba zai kasance wani abu mai sauki ba,kuma gwamnati za ta nazarce shi daga lokaci zuwa lokaci, ta kuma dakatar da shi idan babu wani ci gaba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.