BBC navigation

Shugaba Felipe na Mexico ya gabatar da jawabinsa na karshe

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:43 GMT
Shugaban kasar Mexico Felipe Calderon

Shugaban kasar Mexico Felipe Calderon na gabatar da jawabi ga 'yan kasar.


Shugaba Felipe Calderon na kasar Mexico, ya gabatar da jawabinsa ta karshe ga al'ummomin kasar gabannin cikar wa'adin mulkinsa a watan Disamba mai zuwa.

Mr Calderon ya kare yaki akan masu safarar miyagun kwayoyi da gwamnatinsa ke yi, sai dai ya amince cewa akwai wasu kura-kuren da aka tafka.

Ya kara da cewa akwai wasu jami'an 'yan sanda da suka keta hakkokin bil'adama, amma ya ce ba kasafai aka rika samun afkuwar hakan ba.

Shugaba Felipe ya kuma zargi Amurka da hannu wajen karuwar tashe -tashen hankulan da ake fuskanta a Mexicon, inda ya ce akasarin bindigogin da ake amfani da su wajen kashe-kashe a kasar an yi fasakwaurinsu ne daga kasar Amurka.

''Mun dauki matakai masu muhimmanci kan kasar Mexico, na tunkarar aikata miyagun laifuka yadda ya kamata.Hakan ya sa Mexico ta fara shiga tafarki madaidaici cike da 'yanci da matakan tsaro.'' In ji Felipe Calderon.

Kasar Mexicon dai ta jima tana fama da kalubalen tashe-tashen hankula, aikata miyagun laifuka da suka hada da kashe-kashe da kai hare-hare tsakanin kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyin da ba sa ga maciji da juna, da ma su kansu hukumomin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.