BBC navigation

Shugaba Barack Obama ya ziyarci Louisiana

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT
Shugaba Obama a Louisiana

Shugaban Amurka Barack Obama a Louisiana

Shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarci Louisiana domin bayar da taimakonsa kan farfado da ta'adin da mahaukaciyar guguwar Isaac ta haddasa a makon da ya gabata.

Mutane dubu dari da ashirin da biyar ne suka kasance cikin rashin wutar lantarki, kwanaki shida bayan da guguwar ta abku, yayin da fiye da mutane dubu biyu da dari biyar suka rasa matsugunansu.

A yayin da yake magana a St John the Baptist Parish, daya daga cikin wuraren da guguwar ta fi abka wa, shugaba Obama ya yi magana da wasu mazauna yankin, yana kuma mai yaba wa ma'aikatan agajin gaggawa, wadanda ya ce sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ba.

A ranar Juma'a ne dai abokin karawarsa na jam'iyar Republican, Mitt Romney ya ziyarci jihar ta Louisiana.

Shugaba Obama kuma ya jaddada matakin gaggawa da gwamnatin tarayyar ta dauka, wanda ya ce an tabbatar da bayar da agajin gaggawa, ta yadda mahaukaciyar guguwar ta Isaac bata haddasa asarar rayukan jama'a ba, yayinda ya ke gane wa idonsa yawan adadin barnar.

''An samu mummnar barna a St John's Parish, sai dai ba shi kadai ne wurin da guguwar ta yiwa ta'adi ba. Mun kuma ga ta'annatin da ta yi a yankin Plaquemines Parish da ma wasu sassan jihar Louisiana da Mississipi.'' In ji Obama

Kana Mr Obaman ya jinjina wa ma'aikatan agajin gaggawa.

''Ina kuma so in mika godiya ta ta musamman ga Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa FEMA, da takwarorinsu na jiha da kananan hukumomi, saboda a baya ba mu ga wani hadin kan da ake da bukata wajen tunkarar irin wannan matsala ba, amma a wannan karo mu gani.''

Ziyarar ta shugaba Obama dai na zuwa ne a ranar jajibirin babban taron kasa na jam'iyar Democrats a jihar North Carolina, wanda zai share fagen makwannin karshe na yakin neman zaben shugaban kasa da za a gudanar a cikin watan Disamba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.