BBC navigation

An kai farmaki kan garin Kismayo na Somaliya

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:12 GMT
Hoton bindigar mayaka a Somaliya

Hoton bindigar mayaka a Somaliya

Yanzu haka dai ana ci gaba da zaman fargaba a garin Kismayo, wanda shi ne mafi girma a Kudancin Somaliya, sakamakon wasu hare hare da ake cewa dakarun kasashen duniya na kokarin na kaiwa da nufin korar dakarun kungiyar 'yan kishin Islama ta al-Shabaab.

Rundunar sojin ruwan Kenya, ta tabbatar da cewar ita ce ta kai hare hare a tashar jiragen ruwan ta Kismayo.

Kakakin ma'aikatar tsaron Kenyan, Kanar Cyrus Oguna ya shaida wa BBC cewar sun dauki matakin ne da nufin kwace tashar daga wajen mayakan Al Shabaab.

Mayakan Al Shabaab, wadanda ke iko da garin kusan shekaru uku da suka wuce, sun fara ficewa daga wasu wurare masu muhimmanci kamar ofisoshin 'yan sanda, da filin saukar jiragen sama, da kuma tashar jiragen ruwa wadda aka yi wa luguden wuta dage cikin teku.

Wasu daga cikin mazauna garin na Kismayo sun fara tattara ina su ina su, suna ficewa, duk kuwa da ana cewa kungiyar ta al-Shabaab na kokarin daukar matakan kare wuraren dake hannunta, da kuma kwantar da hankalin mazauna birnin.

Kungiyar Al Shabaab ta ce dakarun Somalia da na Kenya suna parpagande ne don sun jefa tsoro a zukatan mazauna yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.