BBC navigation

Kamfanin Air Nigeria zai dakatar da zirga-zirga

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 21:14 GMT
Wani jirgin sama

Wani jirgin sama

Kamfanin jiragen sama na Air Nigeria ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen saman sa.

Kamfanin na Air Nigeria ya kuma ce ya sallami da dama daga cikin ma'aikatansa.

Shugaban kamfanin, Mr. Jimoh Ibrahim ya ce an dakatar da zirga zirgar kamfanin jiragen na Air Nigeria ne na wasu watanni tare da sallamar ma'aikatan a sakamakon abinda ya kira, rashin biyayya da sakaci da aiki.

Watanni biyu da suka wuce dai, ma'aikatan kamfanin na Air Nigeria suka gudanar da yajin aiki na tsawon mako guda bisa dalilai da aka ce suna da nasaba da batun lafiyar jiragen kamfanin, wanda ke da yawan ma'aikata kimanin dubu daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.