BBC navigation

Michelle ta nuna muhimmancin Obama

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT

Michele Obama

Uwar gidan Shugaban Amurka Michelle Obama ta yi jawabin bude taron jam'iyyar Democrat, inda ta yi kira ga 'yan kasar su sake zaben Maigidanta a wani wa'adin mulki.

Lokacin da take magana a North Carolina, Mrs. Obama ta bayyana Maigidan na ta a matsayin wani mutum dake tare da Amurkawa masu karamin karfi.

Ta kare shawarar da ya yanke ta bullo da dokar nan mai cike da rudani, ta sauye-sauye ga tsarin kiwon lafiya a matsayin wata hanya ta tabbatar da bayar da dama ga kowa da kowa.

Michelle dai ta nuna fifikon da Barack Obama yake da shi kan abokin karawarsa Mitt Romney.

A cikin jawabin nata mai karfin gaske ta bayyana shugaba Obama a matsayin wanda ya san rayuwar masu kananan karfi, duk da cewa miliyoyi daga cikin 'yan kasar basu da aiyukan yi kuma tattalin arzikin kasar har yanzu yana kokarin farfadowa.

Wakilan da suke wajan babban taron dai suna nuni cewa basu girgiza ba bayan shekaru hudu masu wuya da Shugaba Obama ya fuskanta inda yayi ta kokarin tabbatar da aiyukan da ya sa a gaba tsaka da suka daga bangaren 'yan adawa 'yan Jamiyyar Republican.

Jami'an gudanar da Kamfen sa sun nuna kwarin gwiwa kan zaben amma dai sun yi hasashen fafatawar za'a yi ta kusa da kusa.

Da dukkan alamu dai za a gwabza tsakanin Mitt Romney din na Jamiyyar Repubican da kuma Barack Obama na Democrat ko da yake masu iya magana na cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Sakamakon zaben shine zai nuna wanda yafi farin jini a siyasar kasar ta Amurka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.