BBC navigation

Shugaban Colombia na tattaunawa da FARC

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:40 GMT

Shugaba Santos a tattaunawar Colombia

Shugaban Ksar Colombia Juan Manuel Santos da babbar kungiyar 'yan tawayen kasar FARC sun tsara shirin tattaunawar da suke niyyar yi ta sulhu da nufin kawo karshen rikicin da suka shafe shekaru hamsin suna yi.

Mr Santos yace lokaci ya yi da za a nemi zaman lafiya.

Jagoran kungiyar 'yan tawayen ta FARC wanda aka fi sani da suna Timochenko ya fada a wani sako na video cewar an bude fagen sulhu, yana kuma da tabbacin cewar za a cimma nasara.

Fadar gwamnatin Amurka White House ta yi marhabin da wannan shiri na tattaunawa ta kuma yi kira ga jagoran kungiyar ta FARC da ya kawo karshen abinda ta kira shekaru da dama na ta'addanci da safarar miyagun kwayoyi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.