BBC navigation

Mauritania ta wa Libya Abdallah Al-Sanusi

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:31 GMT
Abdallah Al -Sanusi

Abdallah Al -Sanusi

Gidan Talabijin na Mauritania ya ce,an mika tsohon babban jami'in leken asirin Kasar Libya karkashin mulkin marigayi Kanal Mu'ammar Gaddafi, wato Abdullah Al Senusi ga hukumomi a Libya.

An dai kama shi ne watanni shida da suka gabata a Mauritania ,abinda ya janyo gwamnatin Libyan ta yi ta nanata bukatar a maido da shi zuwa gida.

Gwamnatin Libya na zarginsa da aikata laifuka a zamanin Shugaba Gaddafin.

Tun da aka kama shi watanni shida da suka gabata, hukumomin Libya ke bukatar a maida shi gida dan yi masa shari'a.

Sai dai kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC, ma na bukatar a mika mata shi, ita ma gwamnatin Faransa na bukatar a bata shii ta hukunta shi a kan laifukan da ake zargin sa da aikatawa.

A cewar kafar yada labaran Mauritania, tuni aka mika Abdallah Sanussi ga tawagar 'yan kasar ta Libiya da suka je kasar a jiya talata, sai dai kuma har yanzu babu tabbas a kan ko sun isa da shi kasar ta Libya ya zuwa yanzu.

Wannan dai ana ganin wani koma baya ne ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ba wai dan tana son ta samu nasara a mika mata Abdallah ta yi masa shari'a ba, har wa yau tana son a mika mata dan Kanal Gaddafi Seif al-Islam domin ta yi masa abinda ta kira shari'ar gaskiya a mazauninta da ke Hague.

Sai dai kuma hukumomin Libyan sun ki amincewa da hakan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.