BBC navigation

Alkali ya yankewa babban jami'i hukunci a Chile

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:32 GMT

Jami'an tsaro a Chile

Wani Alkali a kasar Chile ya yanke wa wani babban jami'in 'yan sandan-ciki a zamanin mulkin Janar Augusto Pinochet hukuncin daurin shekaru goma sha-biyar a gidan Yari saboda hannun da yake da shi a kisan wani mai fafutuka.

An samu Janar manuel Contreras ne da laifi a kisan Ramon Martinez wani mai fafutukar neman sauyi dan shekaru ashirin da uku da haihuwa wanda ya mutu a hannun 'yan sanda cikin shekarar 1975.

An gana masa azaba ne sannan aka harbe shi.

Dama dai Janar Contreras din yana gidan Yari bisa wasu laifuka da aka same shi da su na sace wasu mutanen da batar da su da kuma kisan kai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.