BBC navigation

Bankin Turai zai warware matsalar bashin kasashe masu amfani da Euro

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:43 GMT
Mario Draghi

Babban bankin Turai ya sanar da shirin sa na sayen takardun lamuni na gwamnatocin kasashen dake amfani da kudin Euro, wadanda bashi yayi wa katutu.

Bankin ya ce ya na sa ran sayen takardun na wucin gadi zai ceto kasashen daga biyan kudin ruwa.

Ana sa ran ci gaban tattalin arziki a tarayyar turai zai ci gaba da zama mara karfi, yayin da ake ci gaba da fuskantar rashin tabbas a kasuwannin hada-hadar kudade.

Shugaban babban bankin Turai-ECB, Mario Draghi ya bada bayanai, filla-filla game da shirin bankin na sayen takardun lamanin kudi na gwamnatin kasashe 17 masu amfani da kudin bai daya na Euro, a wani matakin rage yawan kudin ruwan da kasashen ke biya na bashin da suke karba.

Kasashen da ke son babban bankin Turan ya sayi takardun lamuninsa, dole ne sai sun nemi kungiyar EU ta ba su tallafin kudaden ceto tattalin arziki kasashensu, sannan kuma su amince a kan cewar za su tsaurara matakai game da kasafin kudinsu.

Mario Droghi kuma ya yi hasashen cewar tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro zai kara yin kasa a bana, amma kuma a shekara mai zuwa tattalin arzikin zai dan habbaka da rabin kashi daya cikin dari.

Duk da haka, shugaban na babban bankin na Turai ya nuna alamun cewar watakila matsalar tattalin arzikin da ta dabaibaye kasashen Turai zai kara muni a nan gaba.

Wannan shirin da Mr Droghi ya bullo da shi, zai taimakawa kasashen Turai kamarsu Spain da Italiya wadanda ke fuskantar matsaloli wajen samar da kudaden tafiyar da harkokinsu.

Hukumar bada lamani ta duniya wato IMF ce za ta taimaka wajen tabbatar da cewar kasashen Turai sun cika sharudan da aka gindaya musu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.