BBC navigation

Al-Senussi ya fara shan tambayoyi

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:15 GMT

Al Sanussi, tsohon shugaban leken asiri na Ghaddafi

Firai Ministan kasar Libya ya yi alkawarin yin adalci a shariar Abdullah al-Senussi, tsohon Shugaban hukumar leken asiri na Mu'ammar Ghaddafi.

Lokacin da yake magana bayan hukumomi a Mauritania sun mika al-Senussin, Firai Ministan Abdur-Rahim el-Keib ya ce a shari'ar da za a yi masa za a yi aiki da ka'idojin kare hakkin dan-adam na kasa da kasa.

Kungiyar kare hakkin Bil adama ta yi zargin cewa ba za a yi wa Al Senussin adalci ba a Libya inda ta yi kira da a mika shi ga Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta Duniya dake Hague

Da ma kotun na neman Al Senussi ruwa a jallo kan zargin da ake masa na aikata laifukan yaki a boren da wasu 'yan kasar suka yi a bara, wanda ya yi sanadiyyar hambarar da Marigayi Kanal Gaddafi.

Al Senussi dai mutum ne wanda yake da bayanan sirri da dama na kasar gami da hulda da kasashen ketare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.