BBC navigation

An yi taho mu gama a kusa da Benghazi na Libya

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:06 GMT
Wani hubbaren da aka rusa kwanan baya a Libya

Wani hubbaren da aka rusa kwanan baya a Libya

Jami'ai a Libya sun ce an kashe mutane uku a wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin mazauna wani gari da ke kusa da birnin Benghazi, inda masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama suka yi yunkurin rusa hubbaren wata darikar Sufaye.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce mutanen garin ne suka fatattaki masu tsattsauran ra'ayin—wadanda ake kira Salafawa—wadanda suka yi yunkurin rusa hubbaren wani waliyyi.

Su dai Salafawa suna ganin wadansu ibadu na Sufaye a matsayin bidi'a.

Libya dai na da dadadden tarihin bin darikun Sufaye, wadanda masu nazari suka ce suna kara fuskantar barazana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.