BBC navigation

Kungiyar kamfanonin sadarwa a Najeriya ta yi taro

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:22 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Kungiyar kamfanonin sadarwa na Najeriya ta gudanar da wani taro a birnin Lagos don tattauna matakin da ya kamata ta dauka bayan da aka kai jerin hare-hare a kan turakun sadarwa a wasu sassan arewacin kasar.

Bayan taron dai kungiyar ta ce mambobinta ba su da niyyar dakatar da ayyukansu a sassan da aka kai hare-haren.

A wata hira da ya yi da BBC kafin fara taron, shugaban kungiyar kamfanonin sadarwar, Gbenga Adebayo, ya yi karin bayani a kan abin da taron zai duba:

“Za mu tattauna ne a kan kalubalen da muka fuskanta a wadansu sassan arewacin Najeriya, mu yi nazari a kan abin da ya faru, sannan mu fitar da matsaya a kan matakin da ya kamata mu dauka nan gaba”.

Tambaya: To rahotanni sun ce kuna tunanin dakatar da ayyukanku a sassan da aka kai wadannan hare-hare a arewacin Najeriya....

“Ba gaskiya ba ne—babu wani abu mai kama da dakatar da ayyuka a ko wanne bangare na Najeriya, kuma ba a tattauna a kan wani abu mai kama da haka ba.

“Abin da ya faru shi ne an lalata wadansu daga cikin kayan aikinmu a arewa, amma kungiyarmu ba ta yanke shawara a kan matakin da za ta dauka ba.

“Za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu, kuma ba mu yanke shawara a kan dakatar da ayyukanmu a ko wanne sashe na kasar ba”.

'Hare-haren sun yi ta'adi matuka'

Tambaya: Ko wacce shawara kuke sa ran wannan taro naku zai yanke a kan wannan al'amari?

“Za mu yanke shawarar ce bayan taron, amma ba zan iya cewa ga abin da zai biyo bayan taron ba, saboda muna bukatar mu fahimci tasirin abin da ya faru a kan turakun na sadarwa, sannan mu san mai zai faru daga nan.

Tambaya: To ko kun samu damar tantance irin ta'adin da aka yi wa wadannan turakun naku?

“Muna da rahotannin cewa abin ya shafi tashoshin sadarwa fiye da ashirin da biyar da kuma ofisoshin wasu daga cikin mambobinmu, amma ba mu da cikakkun bayanai.

“Har yanzu muna tattara bayanai, amma dai mun san ta'adin mai yawa ne matuka a wannan sashen na kasar”.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.