BBC navigation

Kotu a Pakistan ta ba da belin Rimsha Masih

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:00 GMT
Masu zanga-zangar neman a soke dokar sabo a Pakistan ranar 30 ga watan Agusta

Masu zanga-zangar neman a soke dokar sabo a Pakistan ranar 30 ga watan Agusta

Wani alkali a Pakistan ya bayar da belin yarinyar nan ’yar shekaru goma sha hudu wadda ake zargi da laifin aikata sabo.

Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama a kasar ta Pakistan sun yi murna da umurnin bayar da belin yarinyar, Rimsha Masih.

Makwanni uku da suke wuce ne dai wadansu makwabtan yarinyar Musulmi suka zargi Rimsha, wacce Kirista ce, da kona Alkur'ani mai tsarki, abin da kuma ya janyo aka tsare ta kuma ake tuhumar ta da batanci ga addini.

Rimsha dai ta kasance a tsare a gidan kaso tun wancan lokacin duk da cewa rahotanni na nuna alamun tana da matsalar fahimta.

Shugaban Cocin Katolika a Islamabad da Rawalpindi, Bishop Rufin Anthony, ya bayyana cewa: “Matakin ya yi kyau, saboda Kiristoci na ganin cewa an yi adalci, kuma wannan yarinyar, kamar yadda mutane suka fahimta, ba ta aikata laifin ba. Don haka bai kamata a daure ta ba a gidan kaso”.

Shi kuwa shugaban kungiyar Kiristoci ta All Pakistan Christian Alliance, Robinson Asghar, jinanawa al'ummar Musulmin kasar ya yi.

“Muna godiya ga shugaban addinin Musulunci da abokanmu Musulmi, wadanda suka ba mu goyon baya.

“Mun godewa kowa, kuma muna tunanin cewa gaskiya ta yi halinta”.

A halin yanzu kuma hadaddiyar kungiyar Kiristocin ta Pakistan ta ce za ta tsaya wa Rimsha Masih, amma dai nan gaba dole ne ta fuskanci shari'a don ta kare kanta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.