BBC navigation

Amurka za ta sa kungiyar Haqqani cikin 'yan ta'adda

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:55 GMT
Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Gwamnatin Amurka na shirin ayyana kungiyar Haqqani mai mazauni a Pakistan a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Ranar Juma'a sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta amince da daukar wannan mataki a hukumance.

Hakan dai na nufin kungiyar ta Haqqani za ta fuskanci takunkumin kashe kudade daga Amurka.

An dai zargi kungiyar da hannu a hare-haren da mayakan sa-kai ke kaiwa a gabashin Afghanistan da ma babban birnin kasar, Kabul.

Sai dai kuma wadansu masharhanta sun ce daukar matakin ka iya gurgunta muhimmiyar dangantakar da ke tsakanin Washington da Pakistan ta fuskar tsaro.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.