BBC navigation

Alkaluman rashin aikin yi ba su gamsar ba —Obama

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:47 GMT
Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka

Yayinda yakin neman zabe ke kara zafafa kafin zaben shugaban kasa a Amurka a watan Nuwamba, Shugaba Barack Obama ya ce alkaluman da ke nuna yawan wadanda ba su da aikin yi a kasar na baya-bayan nan ba su gamsar ba.

Mista Obama ya shaidawa wani taron gangami cewa har yanzu tattalin arzikin kasar ba ya samar da ayyukan yi cikin hanzari yadda ya kamata.

Rahoton na yawan ayyukan da aka samar na wata-wata dai ya nuna cewa rashin aiki ya ragu ne zuwa kashi takwas da digo daya a watan Agusta daga kashi takwas da digo uku a watan Yuli, abin da bai taka kara ya karya ba.

An kuma alakanta akasarin ci gaban da aka samu ne da hakura da mutane da dama suka yi, suka daina neman aiki.

Dan takarar jam'iyyar Republican, Mitt Romney, ya ce alkjaluman sun nuna cewa manufofin Shugaba Obama sun gaza.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.