BBC navigation

Zimbabwe bata gamsu da kudaden lu'ulu'u ba

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:14 GMT

Robert Mugabe

Ministan kudi na kasar Zimbabwe, Tendai Biti ya ce bai ji dadi ba da ma'aikatarsa ke samun kaso dan kadan, daga abin da ya yi tsammanin za ta samu na kudin da kasar ke samu daga cinikin lu'u-lu'u.

Kasar Zimbabwe ce kan gaba a jerin kasashen duniya masu arzikin lu'u-lu'u.

Sai dai Mista Biti ya ce kasar ta sa ba ta amfana da wannan arziki.

A wani taron manema labarai, ya ce daga kimanin dala biliyan daya na cinikin lu'u-lu'un tun farkon shekarar nan, kudin da baitul-malin kasar ta karba ba su kai kashi goma cikin dari ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.