BBC navigation

Mahukunta a Birtaniya na gudanar da binciken kisa

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:41 GMT

Francois Hollande da David Cameron

'Yan sandan Birtaniya da Faransa suna shirin gudanar da bincike a London a gidan wani mutum haifaffen Iraqi wanda aka kashe da iyalansa biyu a gabashin Faransa.

Masu binciken na Faransa har ila yau kuma za su yi tambayoyi ga dan uwan Sa'ad Al-Hilli wanda ya musanta cewar babu wata takaddama da ta faru a cikin iyalan na su a kan batun kudi.

Wani jami'in Faransa Laftanar Kanar Benoit Vinneman ya tabbatar da zuwan 'yan sanda na Faransa a Birtaniya da kuma shirin tambayoyin ga dan uwan Saad al-Hilli.

Yace, A gaskiya ma muna da masu bincike uku ne da aka shirya za su je Birtaniyar. Daya ma har ya rigaya ya isa can.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.