BBC navigation

Hu Jintao ya yi alkawarin habbaka tattalin arziki

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:32 GMT

Hu Jintao Shugaban China

Shugaban kasar China Hu jintao ya yi alkawarin cigaba da habbaka tattalin arziki na biyu mafi girma a duniya don tallafa wa farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya.

Mr Hu ya tabbatar wa Shugabanni a taron koli na kasashen yankin Asia da Pacific da ake yi a Vladi-Vostock cewar sannu a hankali China za ta aiwatar da manufofi tare da bunkasa bukatun cikin gida.

Yace nauyi ne da ya rataya ga dukkan kasashen yankin su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta nemi kasashen yankin su janye duk wani shinge dake tarnaki ga ciniki a yankin pacific.

Jami'an Amurka sun ce za su yi marhabin ga kara taka rawar Rasha a yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.