BBC navigation

Hukumomin Hong Kong sun ce ba darasin dole

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:27 GMT
Masu zanga zanga a Sudan

Masu zanga zanga a Sudan

Gwamnatin yankin Hong Kong ta dakatar da shirinta na mayar da wasu darussa kan kishin kasar Sin su zama dole a makarantu, bayan makonni da aka kwashe ana zanga zanga.

Dubban masu zanga zanga ne suka yi dafifi a kofar shiga ofisoshin gwamnati jiya Juma'a da dare, a wata zanga zanga da aka ce ita ce mafi girma ya zuwa yanzu.

An shafe makonni, dalibai a yankin Hong Kong na jagorantar wata zanga zanga domin ganin an soke wani shiri na gwamnati.

Sun ce darussan za a rika koyarwa kan kishin kasa, tamkar cusa masu wasu ra'ayoyi ne, wani kokari ne na koya masu tarihin jam'iyar kwaminisanci ta China, da kuma nuna tsarin jam'iyya daya a matsayin tsari mafi inganci.

Babban jam'in dake shugabancin yankin, C Y Leung na nuna alamun babu gudu babu ja da baya kan shirin, yana cewa darussan zasu taimaka wajen koya ma dalibai sanin tarihi da al'adun kasar Sin a yankin wanda Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka.

Sai dai kwana guda bayan mutane kimanin dubu dari sun yi zanga zanga a kofar shiga ofisoshin gwamnati, sai ya bada sanarwar dakatar da shirin.

Ya ce za a kawo gyara ga shiri, kuma za a baiwa makarantu zabi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.