BBC navigation

Obama da Romney na musayar yawu kan aikin yi

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:04 GMT

Obama da Romney


A yayinda ake ta Kamfe na zaben kasar amurka, Shugaban kasar Amurka dan takarar Jamiyyar democrat da Mitt Romney dan takarar Jamiyyar Republican na musayar kalamai kan rahoton rashin aiyukan yi na wata wata.

Mr Romney dai ya ce Gwamnatin Obama bata tabuka komai ba kan samar da aiyukan yi.

Rahoto na baya bayana nan kan samar da aiyukan yi a Kasar ta Amurka ya nuna cewar aiyuka dubu casa'in da shida ne aka kirkira a watan Agusta, adadain da bai kai yadda ake tsammani ba.

Barack Obama na Jamiyyar democrat kuwa ya yi nuni da labari mai dadi a kamfe din sa na New Hampshire cewa kasuwancin Amurka ya haifar da aiyukanyi a watanni talatin amma rahoton adadin aiyukanyi da aka samar a watan Agusta bai gamsar da shi ba, inji shi akwai bukatar kara kaimi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.