BBC navigation

Takaddama ta kaure a Zimbabwe tsakanin MDC da ZANU PF

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Morgan Tsvangirai,  Praministan Zimbabwe

Morgan Tsvangirai, Praministan Zimbabwe

Yanzu haka dai ana kara shiga wani yanayi na karuwar zaman zulumi a cikin gwamnatin hadakar kasar Zimbabwe, bayan da praminista Morgan Tsvangirai , jagoran jam'iyyar MDC ya kaddamar da yakin neman goyon baya ga daftarin kundin tsarin mulkin kasar, gabanin kada kuri'ar raba gardama.

Mr Tsvangirai ya shaidawa daruruwan magoya bayansa a birnin Harare cewa ya kamata yan kasar ta Zimbabwe su amince da kundin tsarin mulkin, ba tare da sauye sauyen da jam'iyyar ZANU-PF ta shugaba Mugabe ta aiwatar ba.

Shi dai Mr Tsvangirai ya kalubalanci shugaba Mugabe da ya nemi jama'a su ce a'a , idan har ba ya son kundin tsarin mulkin.

Wannan kiki-kaka tuni ta sa kungiyar kasashen kudancin Afrika SADC ta shiga kokarin sasanta bangarorin biyu.

Mr Tsvangirai ya ce sauye sauyen da kwamitin magabata na jam'iyyar ZANU PF ta shugaba Mugabe suka aiwatar sun bar iko mai yawa karkashin ikon shugaban kasa.

Shi dai Mr Tsvangirai na goyon bayan daftarin na yanzu, wanda jam'iyyarsa ke cewa ya takaita ikon shugaban kasa, inda majalisar dokoki zata rika taka rawa sosai.

Mr Tsvangirai na cewa jibi Litinin zai shaida wa Mr Mugabe cewa ba zai amince da koda daya daga cikin sauye sauyen da ya gudanar ba.

Jam'iyyar ZANU PF ta shafe makonni tana aiwatar da sauye sauye ga kundin tsarin mulkin, kuma zai yi wuya, idan zata bada kai.

Wannan jayayya kan kundin tsarin mulkin mai yuwuwa ta janyo tsaiko a yunkurin da ake yi na gudanar da kuri'ar raba gardama a karshen shekara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.