BBC navigation

Mali: an kashe wasu malaman musulunci

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:49 GMT

Sojan Mali sun ce, sun harbe mutum goma sha shida a yankin Segau na tsakiyar kasar bayan motar da mutanen ke ciki ta ki tsayawa a wurin da aka kafa shingen binciken ababan hawa.

Jami'ai suka ce motar ta ci gaba da tafiya duk da harbin gargadi da dakarun kasar ta Mali suka yi.

Rahotanni na cewa wasu daga cikin wadanda aka kashen din malamai ne masu wa'azi daga kasar Mauritaniya, kuma suna kan hanyarsu ce ta zuwa wani babban taro na addini.

Mai yuwuwa sojojin kasar ta Mali sun zaci wadanda ke cikin motar mayaka ne yan kishin Islama wadanda ke iko da galibin arewacin kasar .

Sai dai kuma lamarin ya auku ne a Segou, wanda kuma yana da nisa sosai daga yankunan da ke karkashin ikon 'yan gwagwarmayar Islamar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.