BBC navigation

Zanga-zangar adawa da hana kaciya a Jamus

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:45 GMT

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel

Kusan Musulmi da Yahuwada dari uku ne suka yi zanga-zangar a Bebelplatz dake birnin Berlin na Jamus, inda suke nuna rashin amincewasu da tsarin kasar da ya haramta yin kaciya.

Ba kasafai Musulmi da Yahudawa ke hada kai da nufin kare wata bukata ta su ba.

Cikin watan Yuni ne dai wata kotun yankin dake birnin Cologne ta ce, yin shayi mummunan laifi ne.

Daga nan sai likitoci a duk fadin kasar suka daina yi wa 'ya'yan Musulmi ko Yahudawa kaciya in suka kai su asibiti, suna cewa matakin ya saba ma doka. A kana haka ne ma aka kai karar wani limanin Yahudawa a Bavaria.

Lamarin dai ya janyo suka daga kasashen duniya.

Wakilin BBC ya ce, tuni dai gwamnatin Jamus ta bayyana cewa, zata halasta yin shayin, amma kuma shugabannin Yahudawa da na musulmi sun bayyana fatan cewa, zanga-zangar da suka yi yau zata kara matsin lamba a siyasance ga gwamnatin Jamus akan wannan batu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.