BBC navigation

An zargi al_Muntada da ba Boko Haram kudi

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:50 GMT
Malam Abubakar Shekau

Malam Abubakar Shekau

Rundunar 'yan sandan birnin London ta ce tana ci gaba da bincike dangane da zargin cewa wata gidauniya mai suna Al Muntada da ke London na taimaka wa kungiyar jama'atul Ahlissunnah Lidda'awti wal jihad da aka fi sani da Boko-Haram da ke Najeriya da kudi.

Wani dan majalisar Dattijan Birtaniya ne, David Alton yayi zargin, yana cewa Gidauniyar ta Al Muntada na da alaka da kungiyar Boko-Haram.

Jaridar Guardian ta London ta ce dan majalisar ya bayyana damuwa ne kan wannan batu na ayyukan kungiyar ta Al-Muntada ga minista a ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya, Lord Howell cikin watan Yuli, ya kuma kara btayar da batun ga hukumar kula da kungiyoyin agaji ta Birtaniya, da kuma ga hukumar 'yan sanda ta Birnin London.

Abin da ba a tantancer ba ya zuwa yanzu, shi ne ko kungiyar al-Muntadar da ake yi wa wannan zargi, ita ce mai hedkwata a London ko kuma wata ce ta daban mai irin sunanta.

Kokarin da aka yi na tuntubar hukumomin tsaro a Nijeriya su mayar da martani kan wannan batu ya ci tura ya zuwa yanzu.

A baya dai an taba zargin kungiyar al-Munatada ta London da taimaka ma wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, amma daga baya aka yi watsi da zargin.

Hukumomin 'yan sanda sun ce sakamakon binciken da zasu gudanar shi zai sa su yanke shawarar mataki na gaba da ya kamata su dauka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.