BBC navigation

Yadda aka kashe Osama bin Laden

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:05 GMT

Gidan da aka kashe Osama Bin Laden a Pakistan

A karon farko, tsohon Kwamandan sojojin ruwan Amurka wanda ya wallafa littafi kan yadda sojojin suka kai samamen da ya yi sanadiyar mutuwar Osama Bin Laden bara a kasar Pakistan, ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya faru.

Kwamandan, wanda aka sakaya fuskarsa, kana aka sauya muryarsa, ya shaidawa gidan talbijin na CBS cewa an harbi marigayi Osama Bin Laden ne a kansa lokacin da yake lekowa ta kofar dakinsa.

Wannan dai ya ci karo da ikirarin da ma'aikatar tsaro ta Amurka ta yi cewa an hallaka jagoran kungiyar al Qaeda ne lokacin da ya tsere zuwa dakinsa.

Kwamandan ya bayyana cewa sai da ya share fuskar Bin Laden kafin ya iya daukar hotonsa bayan da aka kashe shi.

Ya ce: ''A lokacin na tabbatar cewa hoton da zan dauka shi ne hoto mafi muhimmanci da na taba dauka a rayuwata, don haka tilas na tabbatar da cewa na dauki hotunan da kyau. Wannan ya sanya sai da na share fuskarsa domin a iya gane cewa shi din ne''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.