BBC navigation

Ana zaben sabon shugaban Somalia

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:01 GMT

Shugaban Somalia, Sheikh Shariff Sheikh Ahmed, tare da Catherine Ashton

'Yan majalisar dokokin Somalia na zaben sabon shugaban kasar.

Daga cikin wadanda ke takarar takarar shugabancin kasar har da shugaba mai ci, Sheik Sharif Sheik Ahmad da kuma Prayim ministansa, Abdiweli Mohammed.

A shekarun da Somalia ta kwashe ba tare da gwamnatin tarayya ba ta yi fama da fari, da 'yan fashin teku, da rikice-rikicen da suka-ki-ci-suka-ki-cinyewa.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru da dama da za a zabi shugaban kasa a cikin kasar ta Somalia.

Ana bukatar adalin shugaba

Zaben sabon shugaban kasar da za a yi a Somalia wani muhimmin mataki ne na kawo karshen sauye-sauyen siyasar da aka kwashe fiye da shekaru ashirin ana yi a kasar.

Tuni dai kasar ta samar da sabon kundin tsarin mulkinta, da Majalisar Dokoki wadanda za a iya cewa matakan ci gaba ne ganin yadda aka yi fama da rashin zaman lafiya a kasar.

Hanyoyin da aka bi har aka kawo zaben shugaban kasar sun kasance masu tsauri.

Sabon Kakakin Majalisar Dokokin kasar, Mohamed Osman Jawari, ya yi kira ga 'yan majalisun dokokin da su zabi mutumin da ya cancanta.

Ya ce: "Ina kira ga 'yan majalisar da su zabi shugaban da ya cancanta, wanda ke da manufofi da suka da ce da jama'ar Somali. Allah ya taimake mu mu zabi adalin shugaba cikin yanayi mai kyau. Dole ne mu samarwa matasan Somalia makoma ta gari''.

Sai dai har yanzu akwai kalubale da dama. Kasar ta rabu gida-gida ta yadda kusan komai a cakude yake game da neman iko.

Akwai masu tayar da kayar baya na wasu kabilu, da 'yan fashin teku, da masu neman mulkin yanki, da kuma wadanda ke da akala da kungiyar Al Qaeda, wato kamar kungiyar Al Shabaab.

Babu daya daga cikinsu da ke son sarayar da ikonsa ga gwamnatin tarayya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.