BBC navigation

An yi kashe-kashe a Tafawa Balewa, Najeriya

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:51 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Jihar Bauchi a Najeriya na cewa ana ci gaba da samun kashe-kashen mutane a yankin Tafawa Balewa a wadansu al’amura masu nasaba da kabilanci da addini.

Ko da maraicen ranar Litinin ma wadansu mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da ranar Lahadi kuma mutum guda ya rasa ransa baya ga shanu da aka kashe.

Rahotanni sun ce wadansu ’yan bindiga ne suka far wa wadansu motoci da suka tashi daga cikin birnin Bauchi zuwa yankin na Tafawa Balewa, suka kuma bude wuta sannan suka kashe mutane biyu nan take kana suka jikkata wadansu uku, daga bisani kuma daya daga cikin wadanda aka jikkatar ma ta cika a asibiti.

Motocin dai na dauke ne da akasari mutanen da suka fito daga kabilar Sayawa wadanda galibinsu mabiya addinin Kirista ne.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya, wato CAN, a yankin na Tafawa Balewa, Pastor Emmanuel Ibrahim Tumi, ya ce tuni aka kai mutanen da al’amarin ya rustsa da su babban asibitin garin Tafawa Balewa, kuma dukkansu na dauke da raunuka na harbin bindiga.

Wannan al’amari dai ya zo ne kwana daya tak bayan wadansu ’yan bindiga sun kashe wani bafulatani a tsakanin kauyen Gitel da garin Tafawa balewa yayin da yake kiwon shanu.

'Yan sanda sun tabbatar

Daya daga cikin shuwagabannin al’ummar Fulani wadanda galibinsu Musulmi ne, Alhaji Aminu Tukur, ya ce bayan da aka kashe bafulatanin aka bar gawarsa, an kuma kashe biyar daga cikin shanun da yake kiwonsu yana mai cewa an dauki gawar aka yi mata sutura.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ta Bauchi, Muhammad Ladan, ya tabbatar da faruwar al’amarin na ranar Lahadi, amma ya ce bai samu rahoto daga jami’ansu dake yankin ba tukuna danagne da faruwar al’amarin ranar Litinin.

Al’ummomin biyu na Sayawa da Fulani dake yankin na Tafawa Balewa sun jima suna rigima tsakaninsu, musamman a kan al’amuran da suka shafi kasa da wadansu batutuwa na tattalin arziki.

Wannan al’amari dai kan dauki salo na addini, saboda galibin Sayawa Kiristoci ne kana galibin Fulani kuma Musulmi ne.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.