BBC navigation

An kashe wani jagoran Al-Qa'ida a Yemen

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:39 GMT
Said Al-Shihri

Said Al-Shihri

Wani Shafin intanet na gwamnatin Yemen ya ce an kashe mutum na biyu mafi girman mukami a kungiyar Al-Qa’ida a kasar.

Shafin na Ma'aikatar Tsaro ya ce dakarun kasar sun kashe Said Al-Shihri a kudancin kasar, inda dakarun gwamnati suka shafe wata da watanni suna fafatawa da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Gwamnatin ta ce an kashe Al-Shihri ne ranar Larabar da ta gabata a wani farmaki da dakarun kasar suka kai a kan masu fafutukar Islama da ke gabashin Hadhramaut.

Wadansu rahotanni na cewa an kashe Al-Shihri ne tare da wadansu mutane shida a wani farmaki da jami'an leken asirin Amurka, wato CIA, suka kai ta hanyar harba musu makami mai linzami daga wani jirgin saman da ba shi da matuki.

Dan asalin Saudi Arabia ne

Shi dai Al-Shihri dan asalin kasar Saudi Arabia ne wanda aka sako shi daga tsibirin Guantanamo shekaru biyar da suka gabata a karkashin wani shiri na kasar ta Saudi Arabia na kokakarin sauyawa masu kishin Islama ra'ayi daga tsauri zuwa sassauci.

Amma daga baya ya shiga kungiyar Al-Qa’ida da ke kasar Yemen.

Ga Amurka hakan ta sanya alamar tambaya dangane da hatsarin da ke tattare da sallamar fursunonin da ake tsare da su a Guantanamo su koma kasashen su.

Ba wannan ne dai karo na farko da rahotanni ke cewa an kashe Sa'id Al-Shihri ba, amma idan hakan ya tabbata, to zai zama abu mai matukar muhimmanci ga gwamnatin kasar da ma Amurka wadda ke yaki da kungiyar Al-Qa’ida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.