BBC navigation

'Amurka ce babbar abokiyar gabar Pakistan'

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:36 GMT

Shakil Afridi

Likitan nan dan kasar Pakistan wanda ya taimakawa Amurka wajen gano maboyar Osama bin Laden ya shaida wa wani gidan talbijin na Amurka cewa Hukumar Leken Asirin Pakistan ta dauki Amurka a matsayin babbar abokiyar gabar ta.

A wata hira da ya yi a gidan yarin da ake tsare da shi a Peshawar, Dakta Shakil Afridi, ya shaida wa gidan talbijin na Fox News cewa jami'an Hukumar leken asirin Pakistan da suka tuhume shi sun ce ya taimakawa babbar abokiyar gabar Pakistan, wato Amurka wacce har ta fi kasar India a wajensu.

Dakta Afridi ya yi bayanin abin da ya kira mulkin kama-karya a kasar, inda ya ce wasu abokan zamansa a gidan yarin sun shaida masa cewa an ba su shawara kan su yi abubuwan da za su hana jami'an leken asirin Pakistan zuwa gidan yarin domin tuhumarsu.

A baya dai, an yi ka-ce-na-ce tsakanin Amurka da Pakistan game da yadda Amurkan ta shigo Pakistan yayin da ta kashe Osama Bin Laden ba tare da sanin mahukuntan Pakistan ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.