BBC navigation

Iyayen yarinyar da aka zarga da sabo a Pakistan na tsoron rayuwarsu

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
Yara zaune a kofar gidan su Rimsha Masih

Yara zaune a kofar gidan su Rimsha Masih

Iyalan wata yarinya Kirista 'yar Pakistan, Rimsha Masih, wadda ke fuskantar tuhumar batanci ga addinin Islama, sun ce makwabtansu Musulmi sun yi barazanar kona su da ransu a cikin gidansu.

A wata hira da BBC ta hanyar wani tafinta, mahaifin Rimsha, ya ce 'yarsa ba ta aikata laifi ba, kuma ya ce rayuwarsu na cikin mummunan hadari;

Ya ce,"Abun da makwatbatanmu suka fada ma na shi ne cewa za su kona mu a cikin gidanmu, tare da yaranmu. Daga bisani kuma, za su kona gidajen sauran Kiristoci."

Ana dai zargin Rimsha din da kona al Kura'ani mai girma, amma a makon jiya, an kama limamin da ya zarge ta, ana mai zarginsa da kulla ma ta sharri ta hanyar saka sashe na alkuranin da aka kona a cikin jakarta.

An dai bada belin Rimsha Masih, bayan ta shafe makonni 3 a gidan yari, amma har yanzu tana fuskantar sharia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.